Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya zargi jam’iyyar APC da shirin yin maguɗi  a zaben da za a gudanar ranar Asabar, 15 ga Agusta.

Gwamnan ya yi wannan zargin ne bayan kalaman tsohon gwamnan jihar, kuma Ministan Albarkatun Ruwa da Adegboyega Oyetola, wanda ya ce APC za ta kwace kujerar gwamnan jihar.

Oyetola, wanda ya sha kaye a hannun Adeleke a zaben 2022, ya ce amincewar da gwamnan ya yi wa Shugaba Bola Tinubu domin wa’adin mulki na biyu a 2027 ba za ta hana APC lashe zaben ba.

Ya kuma ce korafe-korafen da Adeleke ke yi kan yadda ake tsoratar da wasu ‘yan siyasa na nuna cewa gwamnan ya fahimci cewa yana rasa karfin da yake dashi a siyasarsa a jihar.

Amma Adeleke ya bayyana kalaman Oyetola a matsayin barazana ga gudanar da sahihin zabe.

Gwamnan ya ce al’ummar Osun ba za su amince da duk wani yunkuri na magudin zabe ba, yana mai kira ga hukumomin zabe da masu rajin kare dimokuraɗiyya da su tabbatar da an gudanar da zaben cikin ‘yanci da adalci.

Adeleke ya kuma ce zai sake samun nasara bisa goyon bayan al’ummar jihar, yayin da APC ke mara wa Bola Oyebamiji baya a matsayin dan takarar ta.

A bangaren Oyetola kuwa, ya ce APC na da yakinin cewa za ta dawo da kujerar gwamnan Osun a zaben na bana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *