Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sokoto ta sanar da sake fara aikin duba ababen hawa daga ranar Alhamis, 13 ga Agusta, 2026, domin tabbatar da bin dokokin hanya da ƙara inganta tsaro a kan titunan jihar.
Rundunar ta ce za ta fi mayar da hankali kan motocin da ba su da izinin amfani da gilashin mota mai duhu da masu tuki ta hanyar da ta sabawa hanya wato “One-Way”, da kuma motocin da ba su da cikakkiyar rajista.
Haka kuma, rundunar ta ce za a hukunta masu amfani da lambobin mota na bogi ko na jabu da motocin da lambobinsu suka kasance a rufe da lanƙwasa ko kuma ba a iya karantawa yadda ya kamata.
- Tinubu ya ce gwamnati na son ninka gudunmawar da take bayarwa a ɓangaren kiwo fiye da sau biyu
- Syria – An yanke wa Bashar al-Assad hukuncin kisa
Sauran laifukan da rundunar ta ce za ta tsaurara matakan yaki da su sun haɗa da tukin ganganci da ɗaukar kaya ko fasinjoji fiye da kima da rashin bin alamomin hanya da kuma tukin mota ba tare da ingantaccin lasisin tuƙi ba.
Kwamishinan ’Yan Sandan Sokoto, CP Hayatu Hassan Shaffa, ya ce za a gudanar da aikin cikin nuna ƙwarewa da mutunta haƙƙin jama’a. Ya kuma gargadi jami’an da aka tura aikin da kada su ci zarafi da tsoratarwa ko karɓar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba.
Rundunar ta buƙaci masu ababen hawa su tabbatar motocinsu suna da cikakkun takardu, su cire duk wani abin da ke rufe lambar mota, su mallaki ingantaccen izinin gilashin mota mai duhu idan ya dace, sannan su guji tuƙin aron hannu.