
Ademola Adeleke
An haifi Ademola Adeleke a ranar 13 ga Mayu, 1960, a jihar Enugu.
Mahaifiyarsa, Nnena Esther-Adeleke, ’yar kabilar Igbo ce, yayin da mahaifin sa, Raji Adedeji Adeleke, Bayarabe ne
Adeleke ya fara karatun firaimare a Methodist Primary School da ke Surulere, Jihar Legas, kafin ya koma Nawarudeen Primary School da ke Ikere, Jihar Osun.
Daga nan ya halarci Ede Muslim Grammar School a Ede domin karatun sakandare, kafin daga bisani ya tafi Amurka domin ya zauna tare da manyan yayyen sa biyu.
A Amurka, Adeleke ya halarci jami’ar Jacksonville State University da ke Alabama, inda ya karanci Shari’a da nazarin Laifuka da kuma Kimiyyar Siyasa.
Daga baya ya fadada karatun sa a Kwalejin Atlanta Metropolitan State College, kuma ya samu digiri a fannin fannin Shari’a da Laifuka a shekarar 2021.
Ya kasance Babban Daraktan Gudanar wa a wani kamfanin su mai suna Pacific Holdings Limited, daga shekarar 2001 zuwa 2016.
Daga bisani ya yi aiki a kamfanin rarraba kaya mai suna Quicksilver Courier Company da ke birnin Atlanta, Georgia, Amurka.
- Al’ummar Osun adalci kadai suke bukata daga duk wanda aka zaba-Taofeek
- Gwamnati za ta rufe karɓar ra’ayoyi kan dokar kafa ’yan sandan jihohi
- Masu Lura da Zabe na Kungiyar Lauyoyi ta Kasa (NBA) Sun Iso Jihar Osun Gabanin Zaben Asabar
Adeleke ya kuma kasance mataimakin shugaban kamfanin Origin International LLC, wani kamfani da ke Atlanta wanda ke samar da kayan ƙamshi da sinadaran dandano, daga 1990 zuwa 1994.
Ya kuma taba zama shugaban jami’ar Adeleke University, wata jami’a mai zaman kanta da mahaifan sa suka kafa a Ede, Jihar Osun.
Ya fara harkar siyasa a shekarar 2001 tare da ɗan’uwansa marigayi Sanata Isiaka Adeleke, wanda ya rasu a watan Afrilu na shekarar 2017, wanda rasuwar ta sa ta sanya Adeleke shiga sahun fitattun ’yan siyasa a jihar.
Da farko, Adeleke ya kasance memba na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), amma ya fice daga cikin ta ya koma Peoples Democratic Party (PDP) a watan Afrilu na shekarar 2017, bayan samun saɓanin siyasa kan tsarin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.
Ya tsaya takarar zaɓen cike gurbi (by-election) na Sanatan Osun ta Yamma ƙarƙashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a shekarar 2017 inda ya yi aiki a Majalisar Dattawa ta 8, har zuwa shekarar 2019.
A shekara ta 2018 ya bayyana aniyar sa ta tsayawa takarar gwamnan jihar ƙarƙashin jam’iyyar PDP bayan ya doke Akin Ogunbiyi da ƙuri’u bakwai a zaɓen fidda gwani.
A zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar 22 ga Satumba, 2018, Adeleke ya fafata da ɗan takarar APC, Gboyega Oyetola, da kuma Iyiola Omisore na SDP.
INEC ta bayyana zaɓen farko a matsayin wanda bai kammala ba, lamarin da ya kai ga sake kada kuri’a a ranar 27 ga Satumba, 2018, bayan bayyanar sakamako a zagaye na biyu, aka ayyana Oyetola a matsayin wanda ya yi nasara.
Adeleke ya yi kakkausar suka ga sakamakon, inda ya bayyana zaɓen a matsayin wani juyin mulki na siyasa.
Ko da yake Kotun Sauraron Kararrakin Zaɓe da ke Abuja ta ayyana Adeleke a matsayin wanda ya yi nasara a watan Maris na 2019, daga ƙarshe Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Oyetola a watan Yulin 2019.
Adeleke ya sake dawowa a zaɓen gwamnan Jihar Osun da aka gudanar a ranar 16 ga Yuli, 2022.
Ya sake tsayawa takara a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, inda ya doke gwamnan da ke kan mulki, Oyetola, da ƙuri’u 402,979, yayin da Oyetola ya samu ƙuri’u 375,077.
A watan Disamba na shekarar 2025, Adeleke ya sanar da cewa zai fice daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Bayan ’yan kwanaki sai ya koma jam’iyyar Accord, wanda a ranar 10 ga watan Disamba na shekarar ne ta tsayar da shi takarar gwamna a zaben 15 ga watan Agustan 2026.

Bola Oyebamiji
An haifi Bola Oyebamiji a ƙaramar hukumar Irewole, a garin Ikire, Jihar Osun.
Ya fara karatun sa a A.D.C Primary School, Oke-Ada, Ikire, daga shekarar 1971 zuwa 1977.
Daga nan ya ci gaba da karatunsa a Ayedaade Grammar School, Ikire, daga 1978 zuwa 1982, inda ya samu takardar shaidar kammala karatun sakandare.
Oyebamiji ya samu takaddar kamala ƙaramar diploma OND da kuma Babbar Diploma HND a fannin Banki da sarrafa Kuɗi daga kwalejin kimiyya dake birnin Ibadan.
Daga baya yayi digiri na biyu a fannin Gudanar da Harkokin Jama’a a jami’ar Lagos a shekarar 1997.
A shekarar 2004 kuma ya sake samun wani digirin a fannin Kasuwanci daga jami’ar Ado-Ekiti.
Oyebamiji ya fara aikin sa a shekarar 1987 a bankin Wema, inda ya yi aiki a matsayin Mataimakin Manaja.
A shekarar 1998, ya koma bankin Trans-International, Ikeja, Jihar Legas, a matsayin Babban Manaja.
A shekarar 2005, yakoma bankin Spring dake Lagos, a matsayin shugaban bangaren Kasuwanci.
A shekarar 2009 kuma ya koma bankin Enterprise a Lagos, inda anan ma ya shugabanci sashen da ya rike a inda ya bari.
An naɗa shi Babban Jami’in Gudanarwa (MD) na Kamfanin Zuba Jari na Jihar Osun, a shekarar 2012, daga baya aka naɗa shi Kwamishinan Kuɗi.
A lokacin zaɓen shekarar 2018, ya nemi takarar kujerar gwamnan Jihar Osun a ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), amma daga baya ya janye daga takarar.
A lokacin gwamnatin Gboyega Oyetola, Oyebamiji ya sake zama Kwamishinan Kuɗi.
Daga baya an naɗa shi matsayin mai baiwa Ministan Albarkatun Ruwa Shawara na Musamman, sannan aka naɗa shi Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa (MD/CEO) na Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa na Cikin Ƙasa ta (NIWA) a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Najeem Folasayo Salam
An haifi Najeem Folasayo Salam a ranar 8 ga Agusta, 1965, a Ejigbo, Jihar Osun.
Ya rasa mahaifin sa yana da shekara biyu, sannan ya rasa mahaifiyar sa yana da shekara goma.
Daga nan ya koma zama tare da ƙanwar mahaifiyar sa.
Salam ya halarci Ansar-U-Deen Primary School, Ejigbo daga 1975 zuwa 1981.
Daga nan ya yi karatu a Baptist School, Ola daga 1981 zuwa 1986, sannan ya halarci Baptist High School, Ejigbo a shekarar 1986 zuwa 1987.
A shekarar 1989, an karɓe shi a Jami’ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife, inda ya karanci Kimiyyar Siyasa.
A shekarar 2013 yayi digiri na biyu a wannan fanni, sannan a ranar 5 ga Janairu, 2018, ya kara samun digirin a wannan fanni.
Ya fara siyasa ne tun yana ɗalibin jami’a, inda ya shiga harkar ƙungiyar kare haƙƙin ɗalibai, daga bisani ya kasance ɗaya daga cikin mambobin Kwamitin Bita na gyaran Kundin Tsarin Mulki.
Haka kuma, ya shiga kungiyar daliban yankin da ya fito mai suna Ejigbo Local Government Area Students Association (ELGASA), reshen jami’ar Obafemi Awolowo, har ya shugabance ta.
Bayan kammala karatun sa, Salam ya shiga kasuwancin magunguna, kwarewar da ya samu ya sanya shi baiwa al’ummar yankin Ejigbo taimako a harkar lafiya, har aka naɗa shi kansila mai gafaka (Supervisory Councillor) mai kula da lafiya a shekarar 1999.
A shekarar 2002, ya tsaya takarar shugabancin ƙaramar hukuma amma bai yi nasara ba.
A shekarar 2007, ya tsaya takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Osun, kuma an zaɓe shi.
Bayan haka ne ‘yan majalisar suka zabe shi a matsayin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar.
An sake zaɓar shi a shekarar 2015, kuma ya ci gaba da kasancewa Shugaban Majalisar har zuwa shekarar 2018. Hakan ya sa ya kasance ɗaya daga cikin shugabannin majalisa da suka fi daɗewa a wannan matsayi a jihar.
Bayan ya bar Majalisar Dokokin Jihar Osun, Salam ya zama Shugaban Kwamitin Riƙon Kwarya na Ƙungiyar Kakakin Majalisun Dokokin Jihohin Najeriya a shekarar 2012.
Daga baya, ya zama Babban Daraktan Gudanarwa na Sashen Tallace-tallace da Bunƙasa Harkokin Kasuwanci a kamfanin sadarwar (Nigerian Communications Satellite Limited).