Fadar Shugaban Ƙasa ta sanar da cewa wa’adin karɓar ra’ayoyin jama’a kan kudirin dokar sake fasalin tsarin aikin ’yan sanda zai ƙare da ƙarfe 5 na yammacin yau Alhamis, 13 ga Agusta, 2026.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa kuma shugaban kwamitin da ke aikin kudirin, Femi Gbajabiamila, ya ce manufar karɓar ra’ayoyin ita ce a shigar da ƙwarewa da abubuwan da ’yan Najeriya suka fuskanta cikin tsarin dokar.

Ya ce akwai buƙatar a fayyace yadda za a kare ’yan sandan jihohi daga siyasa da yadda za a binciki jami’in da ya aikata babban laifi, da kuma yadda ’yan sandan tarayya da na jihohi za su rika musayar bayanan sirri.

Gbajabiamila ya ce kafa ’yan sandan jihohi na iya kusantar da aikin tsaro ga al’umma, amma ya ce akwai babbar damuwa kan yiwuwar gwamnonin jihohi su yi amfani da su wajen gallaza wa abokan hamayya ko masu zanga-zanga, ’yan jarida ko wasu al’ummomi.

Ya ce kudirin dokar zai tanadi ka’idojin ƙasa kan ɗaukar jami’ai da horaswa da albashi da fansho da kayan aiki da ladabtarwa da amfani da ƙarfi da korafe-korafe da sa ido mai zaman kansa da musayar bayanan sirri.

Sai dai ya bayyana cewa ba za a kafa ’yan sandan jihohi kai tsaye a duk faɗin Najeriya ba, ko da an kammala sauye-sauyen kundin tsarin mulki da dokar.

A cewar sa, kowace jiha da ke son kafa nata rundunar ’yan sanda za ta buƙaci dokar jiha da tsarin hukumomi da kuma kuɗaɗen gudanarwa, tare da cika sharuddan ƙasa kafin fara aiki.

Ya kuma bayyana cewa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya a yanzu ya tanadi rundunar ’yan sanda guda ɗaya a ƙarƙashin Sashe na 214, saboda haka ana buƙatar gyara kundin tsarin mulkin kafin kafa ’yan sandan jihohi ya zama doka.

Ya ce Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta riga ta amince da wasu gyare-gyaren da za su ba da damar kafa Rundunar ’Yan Sandan Tarayya da Rundunonin ’Yan Sandan Jihohi, amma har yanzu ba a kammala dukkan matakan da ake buƙata ba.

Gbajabiamila ya jaddada cewa har sai an kammala tsarin gyaran kundin tsarin mulkin, tare da samun amincewar aƙalla majalisun dokokin jihohi 24 cikin 36, kafa ’yan sandan jihohi zai kasance a matsayin shawara.

Ya ce jihar da ba ta shirya kafa nata rundunar ba za ta ci gaba da aiki da Rundunar ’Yan Sandan Najeriya (NPF).

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *