Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ta karɓi kayan zaɓe masu mahimmanci, tare da tura jami’an tsaro sama da 25,000 Jihar Osun.
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ta Najeriya, ta ce kayan zaɓe masu muhimmanci sun isa jihar Osun, yayin da hukumomin tsaro suka tura jami’ai sama da 25,000 domin tabbatar da zaman lafiya gabanin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar ranar Asabar.
Kayan zaɓen, waɗanda suka haɗa da takardun jefa ƙuri’a da na’urorin tantance masu zaɓe na BVAS, an ce ana tsare da su cikin tsauraran matakan tsaro kafin a kai su ƙananan hukumomi da cibiyoyin rajistar masu zaɓe a faɗin jihar.
Mai magana da yawun shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa , Adedayo Oketola, ya ce hukumar ta kauce wa bayyana lokacin da aka kawo kayan ko yadda za a rarraba su saboda dalilan tsaro,ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne kayan sun isa jihar kuma an adana su cikin aminci kafin fara rabon su.
Hukumar ta kuma ce za ta yi amfani da sama da mambobin masu bautar Ƙasa guda 30,000 a matsayin ma’aikatan wucin-gadi domin gudanar da zaɓen,ta bayyana cewa akwai masu rajistar zaɓe 2,339,233 a jihar Osun, amma har yanzu ba a tantance adadin waɗanda suka karɓi katin zaɓensu na PVC ba bayan tsawaita wa’adin karɓar katunan.