Bola Oyebamiji, ya yi watsi da zargin cewa yana dogaro da “karfin gwamnatin tarayya” domin lashe zaben da za a gudanar ranar 15 ga Agusta.

Dan takarar jam’iyyar APC a Jihar Osun Oyebamiji ya bayyana hakan ne yayin wata muhawara da manema labarai inda ya ce nasararsa za ta dogara ne da kuri’un jama’a, ba wai da tasirin gwamnatin tarayya ko wata hanya ta siyasa ba, “Jama’a ne za su yanke hukunci,” in ji shi.

Oyebamiji ya ce za a zuba jari sosai a bangarorin noma, ilimi da kiwon lafiya, tare da inganta tsaro da walwalar jama’a.“mun kuduri aniyar kawar da yunwa da talauci” in ji shi, ya kuma ce bunkasa kwarewar jama’a da inganta jin dadinsu na daga cikin abubuwan da gwamnatinsa za ta ba muhimmanci.Oyebamiji ya ce bai ga wata hujja da ke nuna cewa gwamnatin tarayya na shirin amfani da karfinta wajen karkatar da zaben Osun ba.

Ya kara da cewa ya kai ziyara kananan hukumomi guda talatin na jihar sau uku yayin yakin neman zabe, inda ya gana da shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki.“Na ziyarci kananan hukumomi  sau uku amma babu wanda ya taba cewa ya ji ana shirin amfani da karfin gwamnatin tarayya,” in ji shi.

A cewarsa, ganawar da ya yi da jama’a ta nuna cewa suna son sauyin gwamnati,ya ce saboda haka ne yake da yakinin cewa zai samu nasara a zaben da za’a gudanar ranar 15 ga watan Agusta.

A halin yanzu, dan takarar na APC ya kuma yi ikirarin cewa kungiyoyi kusan 42 a fadin jihar sun nuna goyon bayansu ga takararsa.Ya ce daga cikin wadanda suka nuna goyon bayan akwai wasu kamfanoni masu zaman kansu da ma’aikatan gwamnati.

Zaben gwamnan Osun zai gudana ne ranar 15 ga Agusta, inda Bola Oyebamiji na APC zai fafata da sauran ’yan takara ciki har da mai neman wa’adin mulki na biyu, Gwamna Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *