Ƙungiyar rajin kare hakkin bil adama ta yi gargadin cewa akwai barazanar tashin hankali a jihar Osun yayin da ake tunkarar zaben da za a gudanar ranar Asabar.
Ƙungiyar ta bukaci hukumomin Najeriya da su dauki matakan gaggawa domin kare masu kada kuri’a da kuma tabbatar da gudanar da zaben cikin lumana da adalci.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, Amnesty ta ce ta samu rahotannin tashin hankali, kama wasu jami’an gwamnatin jihar da kuma zargin shirye-shiryen yin katsalandan domin yin tasiri kan sakamakon zaben.Kungiyar ta ce a kalla mutane 29 ne suka mutu a cikin wasu tashe-tashen hankula guda 73 da aka samu a sassan jihar.
Ƙungiyar ta kuma ce binciken da tawagoginta suka gudanar ya nuna cewa rikici siyasa na kara kamari a wasu wurare, ciki har da Osogbo, da Ede, da Ife, da Oriade, da Ijebu-Ijesha, da Ilobu da Ikire.
- Wane ne sabon shugaban hukumar tsaron Iran Mohsen Rezaei
- Iran ta gindaya sharuɗɗan buɗe Mashigar Hormuz
- Nijar – Sojoji 17 sun mutu a haɗarin
Babban Darakta na ƙungiyar Isa Sanusi, ya bukaci hukumomi su binciki rahotannin tashin hankalin tare da gurfanar da wadanda aka samu da hannu a gaban kuliya,ya kuma yi kira ga jam’iyyu da magoya bayansu da su yi watsi da tashin hankali, su kuma mutunta ‘yancin al’ummar Jihar na zaben shugabanninsu cikin ’yanci.
Ƙungiyar ta bukaci jami’an tsaro da su kasance masu tsaka-tsaki, tare da gujewa duk wani mataki da zai iya nuna cewa suna goyon bayan wata jam’iyya ko dan takara.
Zaben gwamnan zai gudana ne ranar Asabar 15 ga Agusta, yayin da ake ci gaba da samun zafafa fafatawar siyasa tsakanin jam’iyyu da magoya bayansu.