Gwamnan jihar Osun  Ademola Adeleke, ya ce gwamnatinsa ba ta da isassun kuɗaɗen da za ta yi amfani da su wajen sayen ƙuri’un masu zaɓe.

Adeleke ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da al’ummar jihar da aka gudanar ranar Talata, yayin da ake shirye-shiryen zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar ranar Asabar.

Ya ce gwamnatin jihar ta shafe kusan shekaru biyu tana amfani da kuɗaɗen jihar wajen biyan ma’aikatan ƙananan hukumomi, bayan dakatar da rabon kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar.

“Ba mu da kuɗin da za mu yi amfani da su wajen sayen ƙuri’a. Mun kasance muna amfani da kuɗaɗen jihar wajen biyan ma’aikatan ƙananan hukumomi tun bayan da aka dakatar da rabon kuɗaɗensu kusan shekaru biyu da suka wuce,” in ji shi.

Gwamnan ya ƙara da cewa ba ya ganin akwai buƙatar sayen ƙuri’a domin samun nasara a zaɓen, yana mai cewa ayyukan da gwamnatinsa ta gudanar ne za su yi mata kamfen.

Ya ce, “Ba na buƙatar sayen ƙuri’a domin cin zaɓe. Tun daga 2023 nake bai wa ma’aikata tallafin rage radadin rayuwa. Na yi imani cewa ayyukan da muka gudanar za su yi magana a madadinmu.”

A gefe guda, gwamna Adelek3r ya musanta zargin cewa gwamnatinsa ta fi mayar da hankali kan garinsu, Ede, wajen rabon ayyukan raya ƙasa, tare da yin watsi da sauran sassan jihar.

Ya ce zargin da ake yi wa gwamnatinsa na “Edenization” ba shi da tushe.

A cewarsa, gwamnatin tasa ta gudanar da ayyuka a sassa daban-daban na jihar, ciki har da Ile-Ife, Ila-Orangun, Iwo, Osogbo da Ilesa.

“Rahotannin cewa muna mayar da hankali ne kan Ede ba gaskiya ba ne. Jiya ma na ƙaddamar da wata gadar sama a Ile-Ife, alhali ni ba ɗan Ile-Ife ba ne.

“Mun kuma gina tare da faɗaɗa manyan tituna a Ila-Orangun, Iwo, Osogbo da Ilesa, da sauran wurare, a ƙarƙashin wannan gwamnati. Shin zan yi watsi da Ede ne saboda garina ne?” in ji Adeleke.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *