Dan wasan gaba na Najeriya, Taiwo Awoniyi.

Ɗaukacin mahukunta, da ma’aikata, da ‘yan wasa, da kuma magoya bayan kungiyar Nottingham Forest sun yi wa ɗan wasan gaba, Taiwo Awoniyi ban kwana mai cike da farin ciki a ranar Lahadi, bayan ƙungiyar ta tabbatar da cewa ɗan wasan zai koma sabuwar ƙungiyar da ta hauro Gasar Firimiyar Ingila, wato Coventry City.

Ana sa ran za su kammala yarjejeniyar kafin wasansu na farko da Arsenal a ranar Juma’a.

Coventry ta cimma yarjejeniyar kimanin fam miliyan 17 da Forest a ranar Asabar, yayin da suke ci gaba da kashe kudi sosai gabanin dawowarsu zuwa Gasar Firimiyar Ingila.

Awoniyi ya zama ɗan wasan da Forest ta fi saya da tsada yayin da ya koma kungiyar Union Berlin a 2022 kan fam miliyan 17.2. Dan wasan mai shekaru 29 ya zura kwallaye 23 a wasanni 103 da ya buga wa kungiyar din.

Ɗan wasan gaban na Najeriya ya buga wasa sau 3 kawai a kakar da ta gabata, inda ya ci ƙwallaye 4 a wasanni 17 a dukkan fafatawa.

A watan Mayun 2025, Awoniyi ya ta fama da jnya, bayan ya samu matsala a hanjin cikin sa sakamakon karo da sandan raga yayin wasa da Leicester City.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *