Ƙungiyar Azawad Liberation Front (FLA) ta ƴan ƙabilar Tuareg ta saki sojojin Mali guda shida da suka ji rauni a ranar Lahadi, kamar yadda suka bayyana.
Hakan ya faru ne kwanaki uku bayan da ƙungiyar ta saki wasu sojoji da dama, yayin da ‘yan aware da ƙawayen su masu ikirarin jihadi ke ci gaba da yaƙi da gwamnatin sojin Mali.
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta FLA ta fitar tace ta mika sojojin ga wata tawaga daga Kwamitin Ƙasa da Ƙasa ta Red Cross (ICRC).
- Faston Nijeriya ya karrama malamin Addinin Musulunci da yai shekaru 50 yana koyarwa
- Adeleke: Tinubu ya taya ni murna, amma har yanzu ina jiran kiran Oyebamiji
- Zaɓen Osun: Rundunar ‘Yan sandan Najeriya ta nemi afuwar masu zaɓe
Wani jami’in gwamnatin Mali, ya tabbatar da cewa FLA ta saki sojojin Mali shida, inda ya ƙara da cewa wasu daga cikin su na raunuka.
A ranar Alhamis, rundunar sojin Mali ta sanar da cewa an saki sojojinta 82 bayan da aka yi garkuwa da su sakamakon kama su da FLA da mayaƙanta masu kawance da Ƙungiyar JNIM, wadda ke da alaƙa da ƙungiyar Al-Qaeda.
Tun daga ƙarshen watan Afrilu, JNIM da FLA sun ƙaddamar da jerin hare-hare, inda suka kwace birnin Kidal na arewacin Mali tare da kashe ministan tsaron ƙasar.
Haka kuma, sun taɓa kwace garin Anefis na ɗan wani lokaci a lokacin mummunan faɗa da aka yi a farkon watan Yuli, baya ga wasu jerin hare-hare.