Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Edo, Blessing Agbebaku, ya yi murabus daga mukaminsa a daidai lokacin da ake fuskantar barazanar tsige shi daga kujerar shugabancin majalisar.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan majalisar sun fara yunkurin tsige shi kafin ya yanke shawarar sauka daga mukaminsa.
Ana ci gaba da samun karin bayani kan dalilan da suka sa ya yi murabus da kuma matakin da majalisar za ta dauka na gabagaba
Za mu kawo muku cikakken labarin nan ba da jimawa ba.