Rundunar ’Yan Sandan Jihar Osun ta fayyace rahotannin da suka shafi harba hayaki mai sa hawaye a mazaɓa ta 10 dake Modakeke, Ƙaramar Hukumar Ife East, inda ta ce lamarin ya faru ne sakamakon sakacin wani jami’in ɗan sanda da ke ƙoƙarin yin bayan gida.

Rundunar ta yi wannan bayani ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X a ranar Asabar, bayan da rahotanni da bidiyoyi suka bazu a shafukan sada zumunta cewar wani ɗan sanda ya harba tiyagas kan masu kaɗa ƙuri’a.

A cewar rundunar, lamarin bai faru a kowace rumfar zaɓe ba, sai dai a wata rumfa da ake tantance bayanan masu zaɓe, kuma bawai da gangan yayi hakan ba.

’Yan sandan sun bayyana abin da jami’in ya aikata a matsayin abin rashin jin daɗi, tare da cewa hakan bai dace da ƙa’idar da ake tsammani daga jami’an rundunar ba.

Rundunar ta ce ta kama jami’in nan take, yayin da take faɗaɗa bincike da kuma tattara ƙarin bayanai da suka kai ga afkuwar lamarin.

Haka kuma, rundunar ta yi watsi da zargin cewa an yi hakan ne da nufin hana masu cancantar kaɗa ƙuri’a yin amfani da damar su ta zaɓe.

Rundunar ta nemi afuwar ’yan ƙasa masu bin doka da kuma masu ruwa da tsaki a harkar zaɓe waɗanda wataƙila lamarin ya shafa ko ya jefa cikin damuwa.

Ta kuma tabbatar wa jama’a cewa jami’in da abin ya shafa zai fuskanci matakin ladabtarwa da ya dace, bisa ƙa’idojin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya.

Rundunar ta ƙara jaddada aniyarta ta tabbatar da cewa zaɓen gwamnan Jihar Osun da ake gudanarwa ya kasance cike da ’yanci, adalci, sahihi, cikin lumana kuma ya ƙunshi kowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *