Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da jami’an tsaro su tabbatar da an gudanar da zaɓen gwamnan Osun cikin lumana da gaskiya da adalci.

A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya buƙaci masu kaɗa ƙuri’a su fito su gudanar da haƙƙinsu na ɗan ƙasa, tare da guje wa duk wani abu da ka iya kawo cikas ga zaman lafiyar zaɓen.

Shugaban ya kuma umarci babban sufeton ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da ke aikin zaɓen da su tabbatar da cikakken tsaro a rumfunan zaɓe, tare da kare jami’an INEC da masu kaɗa ƙuri’a daga barazana ko tsoratarwa.

Tinubu ya ce sakamakon zaɓen gwamnan Osun dole ne ya nuna ra’ayin al’ummar jihar, yana mai buƙatar INEC ta yi amfani da wannan zaɓe na musamman a matsayin gwaji na shirinta gabanin babban zaɓen 2027.

A zaɓen na ranar Asabar, yan takara 15 ne ke fafatawa, ciki har da gwamnan jihar mai ci, Ademola Adeleke, ɗan takarar APC, Asiwaju Munirudeen Bola Oyebamiji, da ɗan takarar ADC, Najeem Salaam.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *