Dakarun Operation Hadin Kai sun dakile wani hari da mayakan ISWAP suka kai sansanin sojoji na Mandaragírau, a ƙaramar hukumar Biu ta jihar Borno.
Harin ya faru da misalin ƙarfe 2:00 na dare ranar 15 ga Agusta 2026, inda mayakan suka kai farmaki daga ɓangarori biyu. Sai dai sojojin Bataliya ta 162 sun gano harin ta hanyar na’urorin sa ido, tare da tura dakarun da suka dakile masu harin.
- Tinubu ya buƙaci a gudanar da zaɓen Osun cikin lumana da gaskiya
- Zaɓen Osun: Ɗan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar Accord ya nuna ƙwarin gwiwar samun nasara
Rundunar ta ce an kashe da dama daga cikin mayakan, yayin da aka kwato bindigogin AK-47 da harsasai da na’urar harba rokoki RPG da bama-bamai da wasu kayan yaƙi.
Hotunan na’urorin sa ido sun kuma nuna wasu mayakan suna jan gawarwakin abokan aikinsu zuwa yankin Timbuktu Triangle.
Rundunar ta ce babu wani soja da ya rasa ransa ko jikkata a yayin harin.
Operation Hadin Kai ta ce za ta ci gaba da kai hare-hare da dakile ayyukan ‘yan ta’adda domin hana su samun damar gudanar da hare-hare tare da dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.