Yayin da ake ci gaba da kaɗa ƙuri’u a rumfunan zaɓea jihar Osun, rahotanni sun nuna cewa yanzu haka, an kammala zaɓe a wasu rumfunan, har ma an fara ƙidaya ƙuri’un da aka kaɗa.
Rahotanni sun nuna cewa sakamakon zaaɓen a matakin rumfunan zaɓe sun fara fitowa, daidai lokacin da a wasu mazabun ana dab da fara tattara sakamakon.
- Zaɓen Osun: Rundunar ‘Yan sandan Najeriya ta nemi afuwar masu zaɓe
- Sojojin Operation Hadin Kai sun dakile harin ISWAP a Borno
Duk da kuraren da ba a rasa ba, an tabbatar da Zaɓen ya gudana cikin lumana.
Sai dai babban abin da masu sa ido suka koka da shi a bangare jam’iyyun, shi ne amfani da kudi.
Kamar yadda rahotanni suka nuna, a wasu rumfunan ba a samu an tura sakamakon ba ta na’urar BVAS ba.
An ga magoya bayan jam’iyyu na shewa da tafi yayin da aka sanar da yawan ƙuri’u da jam’iyyunsu da kuma ‘yan takarar su suka samu; musamman idan su ne suka samu ƙuri’u masu yawa.