An gudanar da lacca kan tsaron kasa karo na 8 da Karrama wasu Muhimman mutane na shekara-shekara na Jaridar Blueprint a ranar Talata 18 ga Agusta, 2026. A dakin taro na Bola Ahmed Tinubu (International Conference Center), dake Abuja.Taron ya samu halartar manyan jami’an Tsaro da Gwamnati da shugabannin siyasa.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda.
Haka kuma akwai tsohon gwamnan Jihar Neja, Sanata Abubakar Sani Bello.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, shi ma yana cikin manyan baƙin da suka halarci taron da Sanata Abdulazeez Yari, shugaban kwamitin Majalisar Dattawa kan albarkatun ruwa, da mataimakin gwamnan Jihar Enugu, Ifeanyi Ossai.
-
Zaɓen 2027 zai kasance ɗaya daga cikin mafi kyau – Yari
-
Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa a taron bada lambobin girma na Blueprint karo na 8.
Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Andoma na Doma, Alhaji Dr Ahmadu Aliyu Ogah Onawo wanda ya wakili ci Etsu Nupe.
Taron ya kasance wani dandali na tattauna matsalolin tsaro da cigaban ƙasa da karrama wasu mutane bisa gudummawar da suka bayar.