Imam Abdullahi Mai Shayi, Limamin masallacin Jumma’a na Jabi Garage da ke Birnin Tarayya, ya yi watsi da zargin da Shelkwatar ’Yan Sanda na Abuja ta yi da ke cewa ɓatagari na amfani da yara almajirai don ruɗar masu ababen hawa a wuraren cunkoso don yi wa direbobi sata.
Shelkwatar ’yan sandan wadda ta nuna damuwa kan lamarin, ta yi zargin cewa ɓatagarin suna baiwa yaran kuɗi daga #500 zuwa #1,000 domin ɗauke hankalin direbobi yayin da suke sace kayayyaki masu daraja daga cikin motoci.
Da yake tattunawa da gidan Rediyon Blueprint a ranar Jumma’a, 21 ga watan Augustan 2026, Malam Abdullahi ya ce akwai buƙatar jami’an ‘yan sanda su iya tantance yara almajirai masu koyon karatun allo da kuma yara waɗanda ke gararanba akan tituna.
-
Ana amfani da almajirai a Abuja don yi wa masu ababen hawa sata – ‘Yan sanda
-
Hukumar Tsaron Farin Kaya DSS ta cafke wani sojan gona a Abuja
-
Mambobin ISWAP huɗu sun miƙa wuya
“Duk wani shara sai a jingina ta ga almajirai. Haƙiƙanin gaskiya, ni ba zan iya amincewa da ana anfami da yara almajirai ba ta ɓangaren aikata miyagun ayyuka,” in ji shi.
“Yaran da ake irin wannan abu da su ba almajirai masu karatun allo ba ne. Almajirai da bam, yara ƙanana dabam wadanda ake koyawa ta’addanci. Don ka ga yaro ba tare da iyayensa ba, bashi ne zaka ce wai almajiri ba ne.
“Shi almajiri yana nan da suffan sa na almajirci, yana da lokacin da malaminsa ya bashi na karatu, da na tafiya bara, da kuma lokacin dawowa amma irin waɗannan yaran wani na iya kwana biyu ko uku be koma gidan iyayensa ba.”
Malamin ya ƙara da cewa, zai yi wuya ɓatagari su iya amfani da almajirai masu koyon karatu don haɗa baki dasu a yiwa masu ababen hawa fashi saboda a cewarsa, almajirai basa mu’amala da ɓatagari ballantana har a haɗa baki da su don zaluntar mutane.