Har yanzu ba a samu wata sanarwa a hukumance dangane da halin da Shugaba Paul Biya na Kamaru ke ciki ba, bayan dawowar sa gida daga kasr Switzerland.

Wani mai Sharhi kan al’amuran da suka shafi kasashen Kamaru da Chadi da Nijar ne ya furta hakan a zantawar sa da Blueprint Radio, game halin da ake ciki a kasar, bayan dawowar shugaba Paul Biya gida daga abin da fadar shugaban kasar ta kira ‘gajeren hutu na sirri’.

Abubakar Sa’ad Ganye ya ce har yanzu fa akwai rufa-rufa game da halin da lafiyar Shugaba Paul Biya ke ciki, domin a cewar sa, ba fito fili a hukmance an fayyace wa ‘yan kasa wane irin hali shugaban ke ciki ba.

Ya kara da cewa bugu da kari, an hana ‘yan jarida su gana da shi, ballantana a samu wani bayani daga gurin su.

Game da ko ana zanga-zanga a kasar ta lafa, da yake shugaban ya sawo gida, Abubakar Sa’ad Ganye ya ce ba za a iya cewa ta lafa baki daya ba, domin sai abin da shugaban adawar kasar Isa Ciroma Bakari, wanda ke gudun hijira a kasara Gambiya a yanzu, ya ba da umurni abin da za a yi, musamman a yankunan da yake da rinjaye magoya baya.

Sai dai mai sharhin ya ce ba za a iya fadar me ce ce makomar Kamaru ba yanke take, idan akai la’akari da irin rarrabuwar kan da ake da shi a kasar tsakanin Kudanci da Arewacin kasar dama cikin fadar shugaban kasar, inda ya ce akwai masu son a nada dansa a matsayin mataimakinsa, don ya zamo wanda zai gaje shi; kuma a gefa guda akwai masu ganin su suka fi cancantar su gaji shugaban koda ta ASllah za ta kasance.

Za dai a iya tunawa cewa, yayin da Paul Biya ke waje, sakamakon korafe-korafen da aka samu na cewa babu jagoranci a kasar, ‘yan majalisu sunshigar da kukaga Kotun Tsarin Mulki don tayi amfani da tanadin tsarin mulki na ayyana kujerar shugaban kasar a matsayin wacce babu kowa a kanta, abin da zai jawo nada Shugaban majalisar a matsayin shugaban riko.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *