Gwamnatin Tarayya ta ayyana Gwamnatin Tarayyar ta ayyana Talata, 25 ga watan Agustan 2026, a matsayin ranar hutu ta kasa domin bikin Maulidin bana, Domin murna da zagayowar rabar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).
A madadin gwamnatin tarayya, Ministan Harkokin Cikin Gida, Hon. Olubunmi Tunji-Ojo, ya sanar da hutun tare da mika sakon taya murna ga Musulmi a Najeriya da ma wadanda ke zaune a kasashen waje.
A cikin wata sanarwa da Dakta Magdalene Ajani, Babbar Sakatare a Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, ta sanya wa hannu, ministan ya ce: “Kowace ranar Idi-el-Maulidi tana ba mu damar tunawa da koyon darussa daga rayuwar da ta ginu kan tausayi, tawali’u da kuma yi wa al’umma hidima.”
Ya ƙara da cewa, ya kamata wannan lokaci ya zama na yin addu’o’in haɗin gwiwa domin samun zaman lafiya da haɗin kan ƙasa, yana mai cewa haɗin kan Najeriya nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa.
Tunji-Ojo ya kuma buƙaci ’yan ƙasa da su gudanar da bikin cikin natsuwa da mutunta juna, tare da yi wa al’ummar Musulmi fatan samun Idi mai cike da farin ciki da zaman lafiya.
Ya sake jaddada aniyar gwamnatin yanzu na kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa a faɗin ƙasar, tare da tabbatar da dorewar zaman lafiya a kowane lokaci.