Rundunar ’yan sandan Najeriya ta ƙaryata zargin da sanannen mai amfani da dandalin sada zumunta Martins Vincent Otse wato VeryDarkMan, ya yi na cewa jami’an ‘yan sanda na haɗa baki da masu garkuwa da mutane a shingayen bincike.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Ani Iniedu, ya fitar a ranar Alhamis a Abuja, ya bayyana cewa zargin ba shi da tushe, kuma na neman ɓata sunan rundunar a idon duniya.

Sanarwar ta ce jami’anta da ke kan hanyoyi suna aiki ne domin kare rayuka da dukiyoyi, da kuma daƙile duk wani yunƙuri na ɓata-gari, ba wai ba su bayanai kan matafiya kamar VerydarkMan yayi iƙirari ba.

A Jawaban VeryDarkMan yayin taron Ƙungiyar Lauyoyi ta kasa a birnin Fatakwal ranar Litinin, ya yi zargin cewa jami’an ’yan sanda da ke shingayen bincike a manyan hanyoyi na baiwa masu garkuwa da ‘yan bindiga bayanan matafiya, domin a sace su a karɓi kuɗin fansa.

Akan haka ne rundunar ta gayyaci Matashin ya bayyana gaban ta domin gabatar da hujjojin da yake da su da zu taimaka wajen gudanar da bincike, inda tayi alkawarin daukar hukunci mai tsanani akan duk jami’in ta da aka tabbatar da zargin akan sa.

Rundunar ta buƙaci al’umma da su riƙa amfani da kafofin sadarwa cikin tsari da taka tsan-tsan, domin kaucewa bata suna ko kuma yada zantuka marasa tushe da ka iya kaiwa ga fuskantar hukunci mai tsanani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *