Tawagar ‘yan wasan kasa da shekaru 20 ta Najeriya, Flying Eagles, sun samu gurbin buga wasan kusa da na karshe na Gasar WAFU B U20 bayan doke Togo da ci 3-0 a wasansu na biyu na Rukunin B da suka buga a Yamoussoukro, da ke kasar Ivory Coast, ranar Alhamis.
Flying Eagles sun ci gaba da kyakkyawan salon wasa da suka fara da shi bayan doke Black Satellites na Ghana da ci 4-2 a wasan farko.
An tashi rabin farko na wasan babu ci, amma ana dawo wa daga hutu ke da wuya, Najeriya ta zura kwallon ta na farko ta hannun Muiz Adeleke.
A minti na 59, Adeleke ya sake samun nasarar kara zura kwallon sa ta biyu a wasan.
Shigowar Abdoulaye Agbejoye wanda ya canji Adeleke ke da wuya, ya zura kwallo ta uku, inda sakamakon wasan ya koma ci 3-0, kuma a haka Najeriya ta rike wasan har aka tashi.
Najeriya, wadda ta lashe gasar Afirka sau bakwai, za ta kara da Burkina Faso ranar Lahadi, a wasan da ake sa ran zai fi ko wanne zafi.