Jam’iyyar ADC t
a shigar da wata bukatar gaggawa Cif Jojin Najeriya, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, tana neman a sanya Kotun Koli ta gaggauta bayar da hukunci kan daukaka karar da shugabanta Sanata David Mark ya yi.
A wata wasika da babban lauyan jam’iyyar, S.E. Aruwa, ya sanya wa hannu, ADC ta nuna fargabar cewa jinkirin yanke hukuncin zai iya yin sanadiyyar hana ta shiga Babban Zaben da ke tafe.
Karar mai lamba SC/CV/180/2026 ta samo asali ne daga takaddamar shugabancin uwar jam’iyyar dake tsakanin Sanata David Mark da Honorebul Nafiu Bala Gombe tare da wasu mutum hudu.
- Kotu ta dage sauraron bukatar soke rajistar wasu jam’iyyun adawa
- Gaskiya a sadarwa tsakanin gwamnati da talakawa wajibi ce —Ministan Yada Labarai
- Jam’iyyun adawa za su tsayar da dan takarar Shugaban Kasa guda
A makon da ya gabata Kotun Kolin ta saurari daukaka karar, inda ta ajiye ranar yanke hukunci zuwa wani lokaci da ba ta bayyana ba a nan gaba.
Lauyoyin jam’iyyar sun ce Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) tana kokarin aiwatar da wani hukunci na baya-bayan nan da wata karamar kotu ta yanke, wanda zai iya gurgunta damar jam’iyyar na shiga zabubbuka masu zuwa, matukar Kotun Koli ba ta yi magana ba yanzu.
Lauyoyin sun bayyana wannan roko na gaggawa inda suka bukaci Cif Jojin Najeriya ta ba da umarnin fitar da hukuncin cikin gaggawa domin kare hakkin jam’iyyar da tsarin mulki ya ba ta.
Jinkirin yin hakan, a cewar lauyoyin, ka iya haifar mata mummnar asara.
Kawo yanzu dai hankali ya koma kan hukuncin da kotun kolin zata yanke, duk da cewa ba ta riga ta sanar da ranar da za ta raba wannan gardama ba.