Ministan Yada Labarai Mohammed Idris ya ce lambar yabon shaida ce ta amincin da suke tabbatarwa a dukkan tsare-tsaren sadarwa (Hoto: Adnan Suleiman)

Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris, ya ce bude hanyoyin sadarwa a-kai-a-kai kuma babu boye-boye a tsakanin Gwamnati da wadanda ake shugabanta abu ne mai matukar muhimmanci.

Ministan, wanda ya bayyana hakan yayin da ya karbi wata lambar yabo da kamfanin Vanguard Media Limited, mai wallafa jaridar Vanguard, ya ba shi, ya kuma jaddada kudurinsa na bin tsari mafi ingnaci da gaskiya da amana a bangaren sadarwa na Gwamnatin Tarayya.

“Yayin da muke aiwatar da muhimman sauye-sauye a manufofin gwamnati — ciki har da janye tallafin man fetur da sauye-sauye a musayar kudaden kasashen waje da kuma garambawul ga tsarin kashe kudin gwamnati — mun muhimmantar da yin bayani filla-filla da yin magana daya da kuma tsayawa a kan gaskiya.

“Mun kuduri aniyar tabbatar da cewa an sanar da ’yan kasa manufofin gwamnati cikin mutunci da sanin ya-kamata tare da bayyana alfanunsu na tsawon lokaci ga dukkan ’yan Najeriya a koda yaushe”, inji Ministan.

 Mun kuduri aniyar tabbatar da cewa an sanar da ’yan kasa manufofin gwamnati cikin mutunci da sanin ya-kamata tare da bayyana alfanunsu na tsawon lokaci ga dukkan ’yan Najeriya a koda yaushe.

Ya kara da cewa wannan lambar yabo da aka ba shi shaida ce ta jajircewarsa wajen samar da aminci a tsarin yada bayanai game da sauye-sauyen da Gwamnatin Tarayya take aiwatarwa.

“Wannan lambar yabo shaida ce ta amincin da muke kokarin tabbatarwa a dukkan tsare-tsaren sadarwa, wadanda su ne kashin bayan shugabanci kuma ya wajaba [a aiwatar don ya] kara wa al’umma kwarin gwiwa da hadin kai da kuma kyakkyawan fata”, inji shi.

Daga dama: Ministan Yada Labarai, Alhaji Mohammed Idris, Gwamnan Jihar Taraba, Mista Agbu Kefas, Gwamnan Jihar Enugu, Mista Peter Mba, tsohon Gwamnan Jihar Enugu, Cif Jim Nwobodo da maidakinsa Misis Patricia Nwobodo a wurin Bikin Ba Da Lmabar Yabo ta Vanguard (Hoto: Adnan Suleiman)

Alhaji Mohammed Idris ya kuma jaddada muhimmancin rawar da bayar da bayanai na gaskiya kuma a kan lokaci ke takawa a al;amuran tsaron kasa yana nuni da hadin gwiwar da ma’aikatarsa ke yi da hukumomin tsaro da kafofin yada labarai don samar da zaman lafiya.

Ya kuma yaba da rawar da kafofin yada labarai da abokan aikinsa naGwamnati da Ma’aikatar Yada Labarai suke takawa don bunaksa harkar sadarwa a Najeriya.

An dai yi bikin bayar da lambar yabon ne a Eko Hotel & Suites da Victoria Island a Legas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *