Mai Shari'a Joyce Abdulmalik tace wa'adin shugabannin jam'iyyar bai kammala ba tukuna.

Babbar kotun tarayya anan Abuja ta dakatar da hukumar zaɓe ta kasa (INEC) daga amincewa ko halartar kowane taro da kwamitin riko na jam’iyyar ADC tsagin Sanata David ya shirya.

Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta kuma hana tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark, da sauran jiga-jigan tsagin jam’iyyar tsoma baki a cikin harkokin gudanarwa ga shugabannin jam’iyyar na jihohi waɗanda aka zaɓa ta hanyar doka.

Da take yanke hukuncin a wannan Laraba, Joyce Abdulmalik ta bayyana cewa duk da cewa kotu ba ta shiga maganar cikin gida ta jam’iyyu, to amma tana da damar tsoma baki idan aka saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyya ko na ƙasa.

Kotun ta hana INEC amincewa da duk wani taro da tsagin David Mark ya kira, tana mai cewa kwamitin rikon jam’iyyar ba shi da ikon tsarawa ko shirya tarukan jam iyyar a matakin jihohi.

Kotun ta jaddada cewa wa’adin shugabannin jihohi na nan daram, kuma su ne kaɗai ke da ikon shirya tarukan su, kamar yadda sashi na 223 na kundin tsarin mulkin Najeriya da sashi na 23 na kundin tsarin mulkin ADC suka tanadar.

Wannan ƙara dai shugabannin jam’iyyar na jihohi ne suka shigar da ita ƙarƙashin jagorancin Norman Obinna, inda suke ƙalubalantar Jam’iyyar ADC da David Mark, da wasu mutane 3 da kuma hukumar zabe (INEC).

Da yake karin haske game da bukatun da suka shigar a farko, shugaban shugabannin jam iyyar (ADC) na jihohi Hon Kingsley Temitope Orgar, yace suke da hakkin shirya duk wani taro tun daga mazaba zuwa jiha, da zai kai ga babban taro na kasa.

Orgar yace babban abin da ya rage musu kawo yanzu shine sake garzayawa gaban kotu a karo na biyu, domin ta baiwa (INEC) umarnin hulda da su a matsayin halastattun jagororin jam iyyar, wanda zai kai su ga nasarar shiga babban zabe mai gabatowa.

A ranar Talatar da ta gabata  jam iyyar (ADC) ta shigar da bukata gaban babbar jojin kasa inda take rokon tayi amfani da ofishin ta wajen umartar kotuna su gaggauta yanke hukunci akan kararrakin da ke kan jam iyyar, wanda zai bata damar shiga zabe mai gabatowa.

ita dai wannan shari’a babu ruwan ta da batun rikicin shugabanci dake tsakanin Hon Nafi’u Bala da David Mark, matakin da ke nuna tarin matsaloli da suka dabaibaye jam iyyar, yayin da manyan zabukan kasar ke karatowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *