Tsohon Ministan Lantarki na Najeriya, Saleh Mamman, ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna a Jihar Taraba a karkashin jam’iyyar APC, yana cewa ya karbi fom dinsa na neman tsayawa.
Tsohon Ministan ya ce ya yanke shawarar fitowa takara ne domin ceto Jihar daga halin koma-baya da rashin tasiri a harkokin mulki.
Ya kara da cewa Taraba tana da albarkatun kasa da na mutane, amma rashin ingantaccen shugabanci ya hana jihar ci gaba.
- Kotu ta dakatar da INEC daga amincewa da taron ADC
- Majalisar Wakilai ta amince Tinubu ya ciyo bashin Dala Miliyan 516
- Sanata Marafa ya fice daga jam’iyyar ADC
Shirinsa ya hada da farfado da bangaren aikin gona, ilimi, kiwon lafiya, samar da ababen more rayuwa, da kuma bai wa matasa fifiko.
“Wannan tafiya tamu ce baki daya. Ina kira ga duk wani dan jihar Taraba mai kishin kasa da mu hada kai, mu bar maganar rarrabuwa, mu gina jihar da kowa zai ji dadi kuma kowa zai samu kariya,” in ji tsohon ministan.
Wannan yunkuri na Saleh Mamman ya zo ne a daidai lokacin da jam’iyyu ke shirin tunkarar zaben fidda gwani.
Masharhanta na kallon wannan yunƙuri na Sale Mamman a matsayin wata babbar barazana da ka iya raba kan magoya bayan APC a jihar, biyo bayan komwar Gwamna mai ci Agbu Kefas cikin ta.
Duk da cewa bisa al’ada ta siyasa gwamna dake mulki shine jagora a jiha, Gwamna Kefas na mulki ne a zangon farko, kuma zai iya bayyana aniyar sa ta zarcewa a kowane lokaci.
Rahotanni sun inganta cewa gwamnan na biyayya ga magabatan jihar da suka hadar T Y Danjuma, baya ga damawa da manya da ƙananan ƙabilun jihar Taraba a gwamnatin sa.
Yanzu dai kallo ya koma kan yadda zata kaya tsakanin tsohon ministan da kuma gwamna mai ci, a wannan lokaci da jam’iyyun adawa ke nazarin hanyar da zasu bi domin kwace mulki a hannun APC.