Majalisar wakilai ta amince Gwamnatin Tarayya ta ciyo Bashin Dala Miliyan 516,333,007

Majalisar Wakilai ta amince da bukatar Shugaba Bola Tinubu na karbar bashin dalar Amurka miliyan $516,333,007 (dari biyar da sha-shida, da dubu-dari-uku da talatin-da-uku da bakwai)  daga babban bankin Jamus Deutsche Bank AG. Wanda ke da wa’adin shekaru 9 ana biya tare da hutu na shekaru 3.

A zaman ta na ranar Talata majalisar ta sake bijiro da wannan bukata biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin ta na rance da sarrafa basussuka, wanda mataimakin shugaban kwamitin, Abdullahi Rasheed, ya gabatar.

Ana sa ran yin amfani da wadannan kudade ne domin samar da kudaden gudanar da aikin ginin babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry, inda zai bi ta jihohi 7 da suka hada yankin arewa maso yamma zuwa kudu maso yamma.

A bukatar da ta gabatar wa majalisar, Gwamnatin tarayya ta ware kimanin dala miliyan 265 a matsayin nata kason na gudanar da aikin, da ya shafi biyan diyya ga wadanda ayyukan zai shafa da kuma samar musu kayan more rayuwa.

Adadin bashin da gwamnatin tarayya ta ciyo a cikin gida da waje ya zarce dala biliyan 100 tun daga farkon hawan ta a shekarar 2023 kawo shekarar 2026, kamar yadda kiddigar hukumar kula da basussuka ta kasa (DMO) da kuma hukumar kiddiga (NBS) suka wallafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *