Jigilar maniyyatan bana ta koma shiyya-shiyya, kowacce shiyya akwai kmafanin jirgin da zai yi jigilar ta.

Hukumar jin dadin alhazai ta Kasa (NAHCON) ta sanar da cewa za’a fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa kasa mai tsarki ranar 3 ga watan Mayu na shekarar 2026.

Jirgin farko zai tashi ne daga sabon filin jirgin saman Gateway International da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, wanda shi ne karon farko da maniyyatan jihar Ogun za su tashi kai tsaye daga jihar su tun bayan gina filin jirgin.

Sauran jihohin da zasu biyo baya a wannan rana sun hadar da Abuja, Kogi, Nassarawa, Oyo da Legas da kuma birnin Kebbi.

Wata Sanarwa da mai magana da yawun hukumar jin dadin Alhazan ta Najeriya (NAHCON) Hajiya Fatima Sanda Usara ta aikewa menama labarai, tace tuni tawagar likitoci da jami’an lafiya suka sauka a kasar Saudiyya, gabanin fara jigilar maniyyatan.

Sanarwar tace a wannan shekarar hukumar NAHCON ta fitar da tsarin shiyya-shiyya, tare da fidda kamfanin jigila guda da ayyukansa zasu takaita ne a shiyyar, wanda da zarar ya kammala aikin sa ba zai sake dawowa ba.

Sanarwar tayi karin haske game da maniyyacin da ya rasa jirgin shiyyarsa, zai dauki nauyin bin wani jirgin zuwa wata shiyyar, ko kuma jiran lokacin da za a sake tsarin tafiyarsa anan gaba.

Har ila yau dole ne kowane maniyyaci ya tafi tare da rukunin sa na mutane 45, Katinan Nusuk na kowane rukuni suna can suna jiran isowar rukunin su. Saboda haka ake shawartar kowa ya san sauran mambobin rukuninsa kafin ranar tafiya.

A karshe hukumar ta bukaci maniyyata su tabbatar suna da lambobin wayar shugabannin rukuninsu da kuma jami’an jiharsu da za su kasance tare da su a cikin jirgi.

Wannan shine karo na farko da hukumar ta fidda wadannan tsare tsare domin gudanar da ayyukan ta bisa tsari, kamar yadda sauran kasashen musulman duniya ke yi a kasashen su, na fara dauka da kuma dawo da Alhazai akan kari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *