Kotun Kolin Najeriya ta ce shugabancin Kabiru Tanimu Turaki na jam’iyyar hamayya ta PDP ya haramta.
Kotun ta bayyana hakan ne bayan ta yi watsi da karar da tsagin Turakin ya daukaka yana kalubalantar hukunce-hukuncen Kotun Daukaka Kara da Babbar Kotun Abuja da suka yanke cewa Babban Taron PDP na Kasa da aka yi a birnin Badun na Jihar Oyo ya haramta.
Da ya ke bayyana hukuncin Kotun a ranar Alhamis, Mai Shari’a Stephen Adah ya ce taron, wanda tsagin na su Kabiru Tanimu Turaki ya gudanar a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamban 2025 rashin da’a ne ga hukuncin da alkalin Babbar Kotun Tarayya James Omotosho ya zartar.
- Kotu ta dakatar da INEC daga amincewa da taron ADC
- Jam’iyyar ADC ta aika koke gaban Cif Jojin Kasa
- Shugaban Kasa Bola Tinubu ya yanki tikitin tazarce
Kotun ta caccaki tsagin Turaki bisa garzayawa wata Kotun da ba ta da hurumi a kan shari’ar ta bayar da damar gudanar da taron na Badun, don haka ta ce ya haramta.
A cewarta, wannan karan-tsaye ne ga tsarin aikin kotuna.
Galibin alkalan Kotun Kolin da suka saurari karar ne dai suka yi ittifaki a kan korar karar bisa hujjar cewa ba ta da madogara.
Lauyan tsagin Turakin, Paul Erokoro, ne dai ya garzaya Kotun Kolin yana neman ta soke hukuncin Kotun Daukaka Kara da ya haramta Babban Taron.
Sai dai tsagin Nyesom Wike na jam’iyyar da ma tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido sun kafa hujja da cewa taron ya wuce batun takaddamar cikin gida, kin bin umarnin Kotu ne.
Tsagin na Kabiru Tanimu Turaki dai ya gudanar da Babban Taron ne duk da umarnin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar cewa kada a yi, bayan ta samo wani hukunci daga Babbar Kotun Jihar Oyo wadda ta bayar da damar gudanar da shi.
Haramta taron da duka shawarwarin da aka yanke da abubuwan da aka gudanar a wurin ne suka sa shugabancin Kabiru Tanimu Turaki ma ya haramta.
A yanzu dai Turaki da masu goya mishi baya suna da zabin ci gaba da zama a PDP, amma su yi biyayya ga shugabannin da ke samun goyon Wike, ko kuma su fice daga jam’iyyar.
