Wata tawagar magabatan Jihar Filato mai mutum 32 da suka hada da Gwamna Caleb Muftwang da mambobin Majalisar Dokoki da kuma dukkan tsofaffin gwamnonin jihar da suke raye, ta ziyarci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.

Jagoran tawagar, Gwamna Caleb Mutfwang, ya ce ziyarar na nuni da sabon babi na hadin kan al’ummar jihar da aka bude, domin magance matsaloli dake neman mayar da ita baya.

Ya kuma ce wannan ne karon farko da magabatan jihar suka dunkule waje guda domin kulle duk wata baraka dake tsakanin su, ko dai ta siyasa ko ta addini, kuma tsani ne da zai kai  al’ummarsu ga gane cewa lallai jihar ta dauki tafarkin hadin-kai, kuma a kai ake fatan dorawa domin tabbatar da nasara.

Mutfwang ya jaddada cewa shugabannin a wannan karon sun kuduri aniyar goge duk wani bambanci na addini da kabilanci domin mayar da Jihar Filato kan lakabin da ake mata na “Cibiyar Zaman Lafiya da Yawon Bude Ido.”

Shugaba Tinubu da magabatan Jihar Plateau. Hoto: Bayo Onanuga

A nasa jawabin, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce ya ji dadin ganin wannan tawaga, kuma dole Filato ta gode wa Allah magabatanta suna nan a raye kuma har suka yanke hukuncin kawar da ra’ayi gefe guda domin tunkarar matsalar dake neman mayar da jihar su baya.

Tinubu ya ba su shawarar su koma da baya domin kallon matsalolin Jihar da nufin samar da daidato a tsakani.

“Dole ku koma domin nazarin tsohon tsarin zaman lafiyar da Jihar Filato ke kai, ta hanyar duba dukkanin rahotannin tsofaffin kwamitoci da dokokin da aka taba fitarwa kan rikicin jihar, domin zakulo hanyoyin da za’a iya aiwatar da su a yanzu.

“Hakan zai kai ga tabbatar da zaman lafiya da adalci a tsakani, ba tare da la’akari da kabilanci ko addini ba,” inji Tinubu.

Shugaban ya ce zai yi aiki da wakilan Jihar Filato wajen kirkirar ‘yan sanda na jiha.

Daga bisani Gwamnatin Tarayyar ta fidtar a sanarwar bayar da tallafin Naira biliyan 2 ga wadanda hare-haren Angwan Rukuba ya shafa, daga ofishin Ministan Jin-kai Dokta Mohammed Dorro.

Tsofaffin gwamnoni da suke cikin tawagar sun hada da Sanata Simon Lalong da Sanata Jonah David Jang da Cif Joshua Dariye da Sir Fidelis Tapgun; sai sarakunan gargajiya da suka hada da Mai Martaba Sarkin Wase Mohammed Haruna da Gbong Gwon Jos Da Jacob Gyang Buba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *