Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) reshen Jihar Filato ta yi ƙarin haske game da batun kafa Hukumar Hisbah a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, wadda ya janyo hankalin gwamnati kan lamarin.
A ranar Lahadi, gwamnatin Jihar Filato ta fitar da sanarwar haramta kafa Hukumar Hisbah a faɗin Jihar, inda ta bayyana yunƙurin yin hakan a matsayin haramtacce, wanda gwamnati bata amince dashi ba, sannan kuma ba ta lamunta ba.
Da yake zantawa da gidan Rediyon Blueprint Abuja, a ranar Litinin, Sakataren Jama’atu Nasrul Islam reshen Jihar Filato, Dakta Salim Musa Umar, ya ce babu wata ƙungiyar addinin Musulunci da ta ce za ta kafa Hukumar Hisbah a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, inda ya ƙara da cewa masu amfani da kafafen sada zumunta ne kawai suka ƙirƙiro da hotuna akan lamarin.
-
Dakarun soji sun hallaka wani ɗan ta’adda, sun ƙwato bindigogi a Jihar Filato
-
Soji sun kashe manyan kwamandojin ’yan ta’adda biyu a Katsina
-
Asusun X na Rundunar Sojin Najeriya ya sake fuskantar kutse
“Ina tabbatar wa mutani babu wata ƙungiyar addini a Filato da ta fito ta ce tana son za ta yi Hisbah, babu wannan zancen, ba a taɓa yinsa ba kuma baya cikin abunda ake tattaunawa akai,” in ji shi.
“Abin ya fara ne kawai a kafafen sada zumunta wasu suka fito suka yi uniform da taimakon ƙirƙirarriyar fasaha suna cewa sun yi Hisbah a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, sai kuma abun ya karɓu a wajen mutane suna yaɗawa.”
“Ba a kafa Hukumar Hisbah ba tare da doka daga Majalisar Dokokin Jiha ba, kuma gwamnati ba ta yi hakan ba saboda haka mutane ba zasu fito su ce sun kafa Hisbah ba. Abin ya fara kamar wasa sai ya ɗauki hankalin mutane har ya kai ga gwamnati ta fitar da wannan sanarwar.”
Har ila yau, ya shawarci gwamnati da ta dinga gudanar da bincike mai zurfi da zarar al’amari na addini irin wannan ya faru, yayin da ya gargaɗi masu amfani da kafafen sada zumunta da su guji ƙirƙirar ababen da za su janyo rashin jituwa tsakanin al’umma a jihar.
Tun bayan fitar da sanarwar da Gwamnatin Jihar Filato ta yi na haramta ayyuka da kuma kafa Hukumar Hisabah a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, lamarin ke ci gaba da janyo cece kuce a tsakanin al’umma musamman a kafafen sada zumunta inda aka ƙirƙiro da shi.