Rundunar Sojin Najeriya tayi nasarar cafke wasu daga cikin ’yan ƙungiyar masu garkuwar da ke tserewa a kusa da ƙauyen Gaube, a Ƙaramar Hukumar Kuje ta Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Rundunar ta samu wannan nasarar ne bayan wani samame da ta kai a ranar 2 ga Satumba, 2026
Sojojin sun kama mutane biyu da ake zargi da kasancewa cikin ƙungiyar masu garkuwar, tare da kwato bindigar AK-47 guda ɗaya, da kwanson alburusan AK-47 guda ɗaya da kuma harsasai 19 masu tsawon milimita 7.62.
- Sojojin sun kwato kayayyaki a hannun Boko Haram bayan harin kukawa
- NELFUND: Atiku ya yi alkawarin yafe bashi ga daliban Najeriya
- Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda, sun kama albarusai masu yawa
Rundunar ta ce sojojin na ci gaba da gudanar da ayyukan share yankin da bin sawun waɗanda suka tsere domin cafke sauran waɗanda ake zargi da hannu a lamarin.
A wani samame na daban kuma Rundunar Sojin Najeriya ta ceto matar Birgediya Janar Basil Adonkie, mai ritaya, wadda ’yan bindiga suka yi garkuwa da ita a ranar 1 ga Satumba, 2026.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce bayan samun labarin sace matar, sojojin Guards Brigade da Army Headquarters Garrison (AHQ Garrison) sun ƙaddamar da wani samame na haɗin gwiwa, inda suka bi hanyoyi daban-daban da ake zargin masu garkuwar sun bi domin tserewa.
Rundunar ta ce bayan samun sahihan bayanan sirri, sojojin sun bi ta hanyar Aco Estate zuwa Goza Community, inda suka yi arba da masu garkuwar.
Sanarwar ta ce bayan da masu garkuwar suka fahimci irin saurin martanin sojojin da kuma ƙarfin makamansu, sun bar matar suka tsere zuwa cikin daji.
Daga nan ne sojojin suka yi nasarar ceto Mrs Adonkie a ƙauyen Angwan Sabo.