Gwamnatin Jihar Katsina ta amince da haɗe wasu daga cikin makarantun sakandiren kwana na jihar, sakamakon ci gaba da fuskantar ƙarancin ɗaliban da ke yin rajista a wasu daga cikin makarantun tsawon shekaru.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa daga Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandire ta Jihar Katsina ta fitar.

Sanarwar ta bayyana cewa za a haɗa makarantun da abin ya shafa da wasu makarantun da ke kusa da su domin inganta tsarin gudanarwa da amfani da kayan aiki da ma’aikata yadda ya kamata.

Daga cikin makarantun da abin ya shafa akwai GSS Rawayyau da GSS Shema da GSS Shargalle da GGUSS Jibia da GSS Kai-Kau da GSS Rogogo da GSS Fago da GSS Kabomo, waɗanda za a haɗa su da wasu makarantun da gwamnatin jihar ta ware.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa an yi sauye-sauye ga wasu daga cikin shugabanni da ma’aikatan makarantun da abin ya shafa, inda za a tura su zuwa wasu makarantu ko kuma a sake naɗa su bisa sabon tsarin.

Gwamnatin jihar ta ce an ɗauki wannan mataki ne domin magance matsalar ƙarancin ɗalibai a wasu makarantun kwana, tare da inganta ingancin ilimi da gudanar da harkokin makarantu a faɗin jihar.

Jaridar Katsina post ta ruwaito cewa wannan sauyi zai shafi makarantun da suka daɗe suna fama da ƙarancin yawan ɗalibai, yayin da aka umarci hukumomin da abin ya shafa da su ɗauki matakan gaggawa domin aiwatar da sabon tsarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *