Tsohon , ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023 Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya ce babu wani daga cikin manyan abokan hamayyar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 da ke da ƙarfin da zai inganta Najeriya.

Baba-Ahmed, wanda ya kasance abokin takarar Peter Obi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shirin MicOn Podcast a ranar Asabar.

Baba-Ahmed ya ce manyan ’yan takarar sun taɓa kasancewa cikin wasu jam’iyyun siyasa da gwamnatoci a lokuta daban-daban, waɗanda ya zarga da haddasa halin da Najeriya ke ciki a yanzu.

Ya ce: “Abin da zan ba Uncle (Tinubu) shawara shi ne ya shirya ya miƙa mulki ya bar kujerar, amma ba ga mutanen da ke fafatawa da shi ba.”

“Saboda babu ɗayansu da zai inganta Najeriya. Duk mutanen da ke fafatawa da shi sun taɓa kasancewa tare da juna a wani lokaci ko wani — har da Peter Obi. A wani lokaci, yana cikin PDP.”

Tsohon ɗan majalisar ya ce yana fafutukar ganin an samar da “sabuwar Najeriya”, inda ya yi ikirarin cewa shi ne kaɗai cikin manyan ’yan siyasar da ke neman shugabancin ƙasar wanda bai taɓa kasancewa cikin jam’iyya mai mulki ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *