Tawagar Falconets, yayin gudanar da atisaye.

Moses Aduku, Kocin tawagar ‘yan mata ‘yan ƙasa da shekaru 20 ta Nigeria, Falconets, ya bayyana cewa tawagarsa za ta bayar da ƙarfinta a wasan farko na Rukunin ‘F’ na Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata na ’yan ƙasa da shekaru 20 a ranar Litinin, yayin fafatawa da Spaniya a filin wasa na Stadion Sosnowiec.

“Muna da babban buri a wasan mu da Spaniya. Mun shirya da kyau kuma muna fatan dacewa da yin nasara. Babu shakka, ƙasar Spaniya ta na da kyau; kadda mu manta cewa su ne zakarun duniya a matakin manya na maza,” in ji shi.

“Za mu fuskanci wasan kamar wasan ƙarshe saboda muna son yin nasara. Maki 3 za su sanya mu cikin matsayi mai kyau a matakin rukuni.”

Spaniya ta samu gagarumar ci gaba a Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata ta ’yan ƙasa da shekaru 20 a cikin shekaru 8 da suka gabata.

Sun kai wasan ƙarshe a Faransa a 2018. Sannan kuma, suka zo na biyu bayan Japan ta doke su 3-1.

Har wayau, ‘yar wasan Spaniya, Patricia Guijarro, ta lashe kyautar Gwarzuwar ’yar wasa da kuma Takalmin Zinare. Shekaru biyu bayan haka, a ƙasar Costa Rica, a 2020, sun zama zakarun duniya, inda suka ɗauki fansa akan Japan.

Tawagar Falconets ta Najeriya, labarinsu ya yi kama da na Spaniya.

A 2010, Falconets ta kai wasan ƙarshe, ciki har da doke Amurka a bugun fenariti mai ban sha’awa a wasan kusa da na ƙarshe a Augsburg.

Mako guda bayan haka, bayan sun doke Colombia a wasan kusa da na ƙarshe, Falconets ta sha kashi da ƙwallaye 2 a hannun masu masaukin baƙi Germany a Bielefeld, kuma wannan shi ne karo na farko da Falconets ta yi nisa a Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata ta ’yan ƙasa da shekaru 20.

Kamar yadda Patricia Guijarro ta Spaniya ta lashe kyautar Gwarzuwar ’yar wasa da kuma Takalmin Zinare, a Faransa a 2018 kazalika itama, Asisat Oshoala ta Najeriya, ta yi fice a wasan ƙarshe na 2014 a Canada, inda ta lashe kyautar Gwarzuwar ’yar wasa da kuma Takalmin Zinare.

A wasa na biyu na rukuni, Najeriya za ta kara ne da Ƙasar Sin a ranar Alhamis sai kuma New Caledonia a ranar Lahadi, a wasan ƙarshe na rukuni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *