Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga shugabanni da ‘yan ƙasa masu kishin ƙasa da za su ɗora muradin al’umma sama da buƙatun kan su da neman girma, a yayin da ake fafutukar ciyar da ƙasa gaba.
Tinubu ya yi wannan kiran ne a Cocin St. Monica Cathedral na Lutheran Church of Christ in Nigeria (LCCN), da ke Jimeta, Yola, lokacin taron godiya na murnar cikar tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Dokta Boss Mustapha, shekaru 70 da haihuwa.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, wanda ya wakilci Shugaban Ƙasar, ya buƙaci ma’aikatan gwamnati da ‘yan ƙasa da su mayar da kishin hidimar al’umma da amfanin gama-gari a matsayin babban jigo.
Ya ce Nijeriya na buƙatar shugabanni waɗanda za su kasance masu biyayya ga muradun da suka wuce na ci gaban kan su kaɗai.
“Yau, da farko dai, rana ce ta yin godiya. Mun taru ne ba kawai don murnar cika shekaru saba’in ba, a’a, don murnar amincin Allah, wanda ya kare kuma ya azurta Boss Mustapha a lokuta daban-daban na rayuwa.
“Nijeriya na buƙatar maza da mata masu daraja abin da ya fi ƙarfin buƙatun kan su, maimakon haka su mai da hankali ga hidimar al’umma,” in ji Tinubu.
Shi ma da yake jawabi, Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya bayyana Mustapha a matsayin madubin gaskiya da riƙon amana a aikin gwamnati.
Mutfwang ya kuma yi kira da a ƙara samun haɗin kai tsakanin shugabannin siyasa a yankin Middle Belt.
Haka zalika, Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, wanda mataimakiyarsa, Farfesa Kaletapwa George Farauta ta wakilta, ya yabi tsohon Sakataren na SGF saboda gudunmawar da ya bayar wajen gina ƙasa da kuma juriya da jajircewarsa a aikin gwamnati.
Taron godiyar ya haɗa shugabannin siyasa, jami’an gwamnati, ‘yan uwa, abokai da sauran masoya domin taya shi murna.