Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da naɗin Dr. Lawan Ahmed Muhammad Sani a matsayin Sarkin Gumel na 17, kwanaki uku kacal bayan rasuwar mahaifinsa, marigayi Sarkin Gumel Ahmed Muhammad Sani.

Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Bala Ibrahim, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Lahadi, yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyar NUJ ta Jihar Jigawa da ke Dutse, babban birnin jihar.

Bala Ibrahim ya ce: “Bayan gudanar da shawarwari da Majalisar Masarautar Gumel da masu naɗa sarauta, kuma bisa tanadin Dokar Majalisar Masarautun Jihar Jigawa, Mai Girma Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da naɗin Dr. Lawan Ahmed Muhammad Sani a matsayin sabon Sarkin Gumel.”

SSG ya ce naɗin ya fara aiki nan take, domin tabbatar da ci gaba da shugabanci da kuma zaman lafiya da kwanciyar hankali a masarautar bayan rasuwar tsohon sarkin.

Bala Ibrahim ya kuma yi addu’ar Allah Ya jikan marigayi Sarkin Gumel, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ba wa hukumomin gargajiya goyon baya.

Ya ce: “A madadin gwamnati da al’ummar Jihar Jigawa, muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya sanya marigayi Sarki a Aljannatul Firdaus. Gwamnati za ta ci gaba da jajircewa wajen kare da kuma ƙarfafa hukumomin gargajiya a matsayin masu kula da al’adu da haɗin kan al’umma.”

Bala Ibrahim ya ƙare da cewa: “Nan gaba kaɗan, Mai Girma Gwamna zai miƙa sandar ofis ga Sarkin Gumel na 17 a wani bikin da ya dace da matsayinsa. Muna kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su ba gwamnati haɗin kai domin gudanar da bikin cikin lumana da nasara.”

Idan za a iya tunawa dai a ranar Alhamis 3 ga watan satumba tsohon sarkin Alhaji Ahmad Muhammad Sani ii ya rasu a wani asbiti dake Cairo kasar Egypt.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *