Hoto: Aljazeera

Babbar kotun hukunta manyan laifuka a birnin Alkahirar Masar ta yanke wa wata fitacciyar yar jarida mai suna Sarah Khalifa, tare da wasu mutane 11 hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan an same su da laifin tafiyar da kungiyar asiri da safara da sarrafa miyagun kwayoyi.

Sarah Khalifa, mai shekaru 39, wadda ta shahara wajen gabatar da shirin “Mission Impossible” a gidan talabijin mai zaman kansa na Al-Mehwar, ta musanta dukkan zarge-zargen da ake mata.

Yayin da take sharbar kuka a gaban kotu, ta roki alfarma inda ta bayyana cewa iyayenta sun tarbiyantar da ita a kan tafarkin kwarai kuma ba ta bukatar kudin haram.

Masu shigar da kara sun bayyana cewa gungun wadanda aka yankewa hukuncin suna shigo da sinadaran sarrafa miyagun kwayoyin  daga ketare, su raba a tsakaninsu sannan su sarrafawa da kuma rabawa a cikin al’umma.

Gabanin yanke hukuncin, sai da kotun ta nemi shawarar Babban Muftin Masar Dr. Nazir Muhammad Ayyad, kamar yadda dokar kasar ta tanada.

A watan Afrilun shekarar 2025 ma an yankewa yar jarida Sarah Khalifa daurin shekaru uku a gidan yari, bayan samun ta da laifin cin zarafi da daukar bidiyon direbanta ba tare da sanin sa ba.

A tsarin shari’ar Masar, wadanda aka yankewa hukuncin na da kwanaki 60 domin daukaka kara zuwa kotun kolin kasar da ake yiwa lakabi da “Mahkamat al-Naqd.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *