Sporting Lagos ta samu babban nasara a wasanta na biyu na Gasar Firimiyar Najeriya (EuroNPFL), inda ta lallasa Inter Lagos a gidanta, da ci 3-0, a wasan da suka buga a ranar Lahadi.
Sodiq Ayoade da Aliyu Baba da kuma Valentine Ugwu, kowannen su, ya zura ƙwallo daya, yayin da Sporting ta tabbatar da nasara a karawar.
A wani wasan na daban, Barau FC ta samu gagarumar nasarar doke Ranchers Bees da ci 3-1 a wasan da suka buga na ranar Lahadi.
A yanzu, Barau FC ta na matsayi na biyu a teburin Firimiyar Najeriya da maki bakwai bayan doka wasanni uku.
A garin Ilorin, Kwara United ta lallasa Katsina United da ci 3-0, inda a yanzu ta hada maki hudu kuma take matsayi na biyar a teburin Firimiyar Najeriya bayan buga wasanni uku.
Ga cikkkaken sakamakon wasanni da aka buga na ranar Lahadi:
Abia Warriors 2-2 Ikorodu City
Barau FC 3-1 Ranchers Bees
Bendel Insurance 4-2 Kun Khalifat
Inter Lagos 0-3 Sporting Lagos
Kwara United 3-0 Katsina United
Niger Tornadoes 1-1 Plateau United