An kama wata mata a karamar hukumar Rogo ta jihar Kano bisa zargin kashe mijinta, Hafizu Gausu, wanda aka bayyana cewa yana shirin kara auren mata ta biyu.

Wani mazaunin yankin, Auwal Kazagi Rogo, ya shaida wa Jaridar Daily Trust cewa lamarin ya faru ne ranar Juma’a da misalin karfe 7 na yamma a yankin Katsalle na garin Rogo.

A cewarsa, mazauna yankin sun garzaya zuwa wurin da abun ya faru sakamakon jin kukan matar margayin (Gausu) inda ta yi ikirarin cewa an yanka mijinta.

“Da muka isa wurin, mun ga ba a yanka shi ba sai dai an buge shi a kai da wani abu. Yana kwance a cikin jini ya mutu. Har ma da akwai alamar cizo a kunnensa,” in ji Kazagi.

Ya kara da cewa an kira ‘yan sanda nan take kuma bayan sun zo sai suka tafi da gawar don gudanar da bincike.

Kazagi ya kara da cewa ana zargin cewa Gausu ya yi alkawarin zai auri wata mata kwanan nan, don ta zama matarsa ta biyu.

Hakan ya haddasa rikici babu kaukautawa da matarsa, wadda ake zargin ta sha alwashin za ta hana auren sannan kuma dattawa sun shiga tsakanin rikicin, amma rigimar ya ci gaba da wanzuwa.

Kazagi ya ce ‘yan sanda sun kama matar marigayin a matsayin babban wadda ake zargi da aikata laifin.

Mijin kuwa, an binne shi da safiyar ranar Asabar a Rogo bisa yadda addinin Musulunci ya tanadar.

A cewar wata majiya, ma’auratan sun yi aure kusan shekaru bakwai da suka wuce kuma Allah ya albarkace su da ‘ya’ya biyu, kuma ana tunanin cewa a halin yanzu, matar marigayin tana dauke da juna biyu na marigayin.

Majiyoyi a yankin sun ce Gausu har ma ya bukaci iyayen amaryarsa da su janyo ranar daurin auren gaba da watanni biyu saboda irin adawar da matarsa ke nunawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *