Rahotanni daga jihar Kano sun ce wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Alhaji Ahmad Yakubu Ahmad, dagacin kauyen Aujarawar Alkali da ke karamar hukumar Gezawa.
An ce ‘yan bindigar sun kutsa cikin kauyen ne a daren Alhamis, inda suka yi awon gaba da dagacin. Lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin fargaba tare da kara tayar da hankalin iyalai da shugabannin al’umma.
Isma’il ya bayyana sace dagacin a matsayin wani abin takaici da kuma babban koma baya ga zaman lafiya da tsaron yankin. Ya ce lamarin ya kara haifar da damuwa kan lafiyar al’ummar yankin da kuma inda dagacin yake.
-
FCT: ’Yan sandan sun kama mutum 300 a samamen maboyar masu laifi
-
Ƙungiyar CJTF-TF ta nemi gwamnatin tarayya ta amince da ita
Da yake mayar da martani kan lamarin, dagacin gundumar Jogana, Alhaji Abdulkadir Ma’aji, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen ceto dagacin tare da karfafa tsaro a kauyukan da ke cikin hadari.
Alhaji Abdulkadir Ma’aji ya ce wajibi ne jami’an tsaro su kara kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da yin duk mai yiwuwa domin ganin an dawo da dagacin cikin koshin lafiya.
Dagacin ya kuma bukaci mazauna yankin su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da bin doka, tare da bai wa jami’an tsaro hadin kai da bayanan da za su taimaka wajen dakile ayyukan masu laifi. Ya kuma roki jama’a da su yi addu’ar ganin an sako dagacin lafiya.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce zai tuntubi wakilinmu bayan ya samu karin bayani daga jami’an da ke yankin.