Ƙungiyar Citizen Joint Tactical Formation (CJTF-TF) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ba ta cikakkiyar amincewa tare da haɗin gwiwa da ita, a matsayin wata ƙungiya mai taimakawa hukumomin tsaro a cikin tsarin tsaron ƙasar.
Ƙungiyar ta kuma jaddada wajibcin tantance jami’anta tare da ƙaddamar da wani shirin kula da lafiyar al’umma a faɗin jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
- Filato: ‘Yan Sanda sun kama mutum 34, sun kwato bindigogi 10 da harsasai 54
- Yara kanana da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba sun mutu a hannun Hukumar Tsaro ta NSCDC a Jihar Neja
- Atiku ya soki gwamnatin Tarayya kan tsadar rayuwa
Kwamandan Janar kuma Mai Gudanarwa na Ƙasa na CJTF-TF, Tanimu Shehu, ne ya yi wannan kiran cikin wata sanarwa da ya fitar a Jos ranar Juma’a.
Shehu ya bukaci Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Tarayya da Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA) da su yi hulɗa da tsarin tattara bayanan sirri na ƙungiyar ta al’umma.
Ya ce CJTF-TF na da hanyoyin tattara bayanan sirri a birane da yankunan karkara, waɗanda suka fi mayar da hankali wajen tattara bayanai ba tare da amfani da tashin hankali ba.
A cewarsa, haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyar da hukumomin gwamnati da abin ya shafa zai iya ƙarfafa taimakon tsaro a matakin al’umma wajen yaƙi da garkuwa da mutane da ’yan fashi da sauran matsalolin tsaro.