Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON, ta tunatar da maniyyatan aikin Hajjin 2027 cewa kwanaki bakwai ne suka rage kafin cikar wa’adin ranar 26 ga Satumba domin yin rajista da kuma ɗora bayanan maniyyata.

NAHCON ta fitar da wannan tunatarwar ne ranar Asabar ta shafinta na X, inda ta buƙaci maniyyata da sauran masu ruwa da tsaki su kammala rajista da ɗora bayanansu kafin cikar wa’adin.

Wannan tunatarwa na zuwa ne yayin da shirye-shiryen aikin Hajjin 2027 ke ƙara .

A baya, NAHCON ta yi gargadin cewa rashin ɗora bayanan maniyyata kafin ranar 26 ga Satumba na iya jawo rasa guraben da aka ware.

Hukumar ta ce an sanya wa’adin ne bisa jadawalin da aka tsara domin gudanar da aikin Hajjin, ciki har da buƙatun da suka shafi tsarin dijital na Saudiyya wajen sarrafa bayanan maniyyata.

NAHCON ta kuma bayyana cewa ana sa ran kammala tura dukkan kuɗaɗen guraben da aka ware zuwa ranar 2 ga Disamba 2026.

Ta shawarci maniyyata da su biya kuɗaɗen aikin Hajjin ne kawai ta hanyoyin da hukumomi suka amince da su, ciki har da hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi da bankunan ajiyar kuɗin Hajji da aka amince da su da kuma kamfanonin yawon buɗe ido da ke da lasisi.

Kwanaki biyu kafin wannan sanarwar, Saudiyya ta ƙi amincewa da buƙatar Najeriya na ƙarin guraben aikin Hajjin 2027, lamarin da ya bar Najeriya da adadin guraben maniyyata 50,000 da aka amince da su domin aikin Hajjin na shekara mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *