Hukumar Kula da albarkatun Man Fetur na ruwa dana tudu (NMDPRA) ta ce ba ita ce ke kayyade farashin man fetur a gidajen mai ba, tana mai cewa farashin man fetur yana tafiya ne bisa tsarin kasuwa mai ’yanci da tanadin Dokar Masana’antar Man Fetur ta 2021, wato PIA.
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar yayin da ta amince da matsin tattalin arziƙin da ƙarin farashin man fetur na PMS ya jefa ’yan Najeriya, musamman iyalai da ma’aikatan sufuri da ’yan kasuwa.
NMDPRA ta ce ƙarƙashin sashe na 205(1) na dokar PIA, farashin sayar da man fetur da kuma dillalan shi zai kasance bisa tsarin kasuwa mai ’yanci, don haka hukumar ba ta kayyade farashin a gidajen man fetur ko fitar da wani jadawalin farashi na dole ba.
- Kwanaki bakwai suka rage a kammala rajistar Hajjin 2027 – NAHCON
- Ƙungiyar CJTF-TF ta nemi gwamnatin tarayya ta amince da ita
- Cibiyar harkokin kasuwanci ta Abuja za ta fara aiki a Disamba 2027 – Minista
Ta ƙara da cewa sashe na 205(2) zuwa (4) ya takaita sa hannun gwamnati wajen farashin albarkatun man fetur ne kawai a yanayi na musamman inda aka tabbatar da gazawar kasuwa.
A cewar sanarwar, sashe na 216 na dokar PIA ya bai wa NMDPRA ikon hana ayyukan da ke tauye gasa da daidaita farashi tsakanin ’yan kasuwa da kuma cin zarafin rinjaye a kasuwa.
Dangane da samar da man fetur da hana safarar shi zuwa ƙasashen waje, NMDPRA ta ce tana aiki tare da Hukumar Kwastam ta Najeriya da sauran hukumomin tsaro domin ƙara sanya ido a iyakokin ƙasa da kuma dakile safarar man fetur ba bisa ƙa’ida ba.
NMDPRA ta ce tana da yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da Federal Competition and Consumer Protection Commission (FCCPC), inda hukumomin biyu ke gudanar da sa ido tare kan ƙarin farashi ba bisa ƙa’ida ba da haɗa baki wajen farashi da rage adadin man da ake zubawa abokan ciniki da kuma matsalolin ingancin man fetur.
Idan dai za a iya tunawa a cikin ‘yan kwankin nan farashin man fetur ya karu a fadin Najeriya, lamarin da ya kara jefa ‘yan kasa cikin mawuyacin hali.