Ministan Ƙasa na Masana’antu, John Enoh, ya ce Cibiyar Harkokin Kasuwanci ta Abuja, ACE, za ta fara aiki zuwa watan Disamba na shekarar 2027, bayan kammala gininta.
Mista Enoh ya bayyana hakan ne a Abuja, yayin bikin aza harsashin ginin cibiyar da ke ƙarƙashin Hukumar Bunƙasa Ƙananan da Matsakaitan Kamfanoni ta Najeriya, SMEDAN.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Hukumar Haɗin Kan Ƙasashen Duniya ta Koriya ta Kudu, KOICA, ce ke ɗaukar nauyin aikin, yayin da Shirin Raya Ƙasashe na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNDP, ke aiwatar da shi, domin tallafa wa matasa ’yan kasuwa da sabbin kamfanoni a faɗin Najeriya.
- Filato: ‘Yan Sanda sun kama mutum 34, sun kwato bindigogi 10 da harsasai 54
- Yara kanana da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba sun mutu a hannun Hukumar Tsaro ta NSCDC a Jihar Neja
- Atiku ya soki gwamnatin Tarayya kan tsadar rayuwa
Enoh ya bayyana aikin a matsayin wanda ya wuce gina cibiya kawai, yana mai cewa zai samar da dama ga ’yan kasuwa da masu ƙirƙire-ƙirƙire da kamfanoni a faɗin Najeriya su bunƙasa.
Ya ce gwamnatin tarayya ta tabbatar da abubuwan da ake buƙata domin ganin an kammala aikin, yana mai fatan cibiyar za ta taimaka wajen bunƙasa masana’antu da harkokin kasuwanci a Najeriya.
Ana sa ran cibiyar za ta tallafa wa matasa ’yan kasuwa 500 da kuma sabbin kamfanoni 400 a fannonin fasahar kuɗi, da suka hada da FinTech; fasahar ilimi, da EdTech; fasahar kiwon lafiya, HealthTech; da fasahar noma, AgriTech.
Haka kuma, cibiyar za ta samar da tallafi ga ƙananan da matsakaitan kamfanoni a Abuja da wasu biranen arewacin ƙasar da ke kewaye da babban birnin tarayya.