Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki Gwamnatin Tarayya kan matsalar tsadar rayuwa da ƙasar ke fuskanta, inda ya tambayi tsawon lokacin da ‘yan Najeriya za su ci gaba da jure matsin tattalin arzikin.

A cikin wata sanarwa da Babban Mataimakinsa na Musamman kan Sadarwar Jama’a, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya bayyana ƙara taɓarɓarewar matsalar rashin abinci mai gina jiki ga yara a Najeriya a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi nuna girman matsalar tsadar rayuwa a ƙasar.

Ya yi gargadin cewa matsin tattalin arzikin ba ya ƙara takura aljihun iyaye kawai, har ma yana barazana ga ci gaban jiki da makomar miliyoyin yara ‘yan Najeriya.

Sabbin alkaluman da ƙwararrun harkokin abinci mai gina jiki suka gabatar sun nuna cewa kashi 41.1 cikin 100 na yaran Najeriya ‘yan ƙasa da shekaru biyar suna fama da ƙarancin tsayi sakamakon rashin isasshen abinci mai gina jiki, yayin da kashi 19.2 cikin 100 ke fama da matsanancin ƙarancin tsayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *