Wata sanarwa da Kwamandan NSCDC na Jihar Neja, Kwamanda Suberu Siyaka Aniviye, ya sanya wa hannu ta ce an kama mutanen ne tsakanin 15 da 16 ga Satumba 2026, bayen an rufe su sai aka same su sun mutu a ranar 17 ga Satumba, bayan barkewar cuta a ɗakin da ake tsare da su.
Hukumar ta ce an gudanar da samamen kwatsam kan masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, inda aka kama mutane da dama tare da kwato wasu kayayyakin da ake zargin na ayyukan haƙar ma’adinai ne.
Sai dai hukumar ta yi kira ga jama’a da su kwantar da hankula, tana mai cewa jami’an tsaro na aiki tare da hukumomin da abin ya shafa domin gano musabbabin mutuwar mutanen. Sanarwar ta kuma bukaci iyalan waɗanda suka mutu da sauran jama’a su guji duk wani mataki da ka iya haifar da rikici da Karya doka da oda.
-
Ta’aziyyar Bamanga Tukur: Shettima ya jagoranci tawagar gwamnatin Tarayya zuwa Yola
-
Kotun ICC ta yi watsi da ƙarar Sunrise kan gwamnatin Najeriya
NSCDC ta ce har yanzu lamarin na ƙarƙashin kulawa, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro. Ta kuma ce tana da cikakken ƙudurin kare haƙƙin ɗan Adam tare da bin ƙa’idojin ƙasa da ƙasa na kare haƙƙin ɗan Adam, yayin da take gudanar da muhimman ayyukanta da suka haɗa da kare rayuka da dukiyoyi, da kuma muhimman kadarori da ababen more rayuwar ƙasa, domin amfanin al’umma.