Ƙungiyar Obi-Kwankwaso Movement ta ƙaddamar da tsarin yaƙin neman zaɓenta a faɗin Najeriya gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Ƙungiyar ta bayyana kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa mai mambobi 59, wanda ya ƙunshi wakilai daga shiyyoyin siyasa shida na ƙasa, Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma jihohi 36.
Kwamitin ya haɗa da masu gudanarwa na shiyya da jihohi, da kuma daraktoci masu kula da fannoni daban-daban da suka haɗa da tattara magoya baya da harkokin mata da dabarun yaƙin neman zaɓe da tsare-tsare da tsaro da bayanan sirri da harkokin shari’a da gudanarwa da fasahar sadarwa.
- Kotun ICC ta yi watsi da ƙarar Sunrise kan gwamnatin Najeriya
- Saudi Arabia ta ƙi ƙarawa Najeriya kujerun aikin Hajjin 2027
- Ta’aziyyar Bamanga Tukur: Shettima ya jagoranci tawagar gwamnatin Tarayya zuwa Yola
An nada John Ughulu, a matsayin Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen.
An naɗa Suleiman Abubakar a matsayin mai kula da yankin Arewa ta Tsakiya, sai Hashimu Dungurawa a Arewa maso Yamma sai Amadu Gwambe na Arewa maso Gabas da Adebayo Adefolaseye na Kudu maso Yamma; Christopher Ighodaro na Kudu maso Kudu; yayin da El-Shaddai Ikeh zai kula da Kudu maso Gabas.
Ƙungiyar ta kuma naɗa masu gudanarwa a jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja, matakin da ta ce zai faɗaɗa ayyukanta zuwa matakin ƙasa.
Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da Sabo Gashua, Daraktan Tattara Magoya Bayana Ƙasa da Glory Adayi, Daraktar Harkokin Mata da Kabir Yahaya, Daraktan Hulɗa jama’a da Sadarwa da Abdumumini Tijjani, Daraktan Tattara Magoya Baya; da Yusuf Mani, Daraktan Ayyuka na Musamman.
An naɗa Farfesa Charles Nwekeaku a matsayin wanda zai kula da tarukan jama’a na Kudu maso Gabas, sannan Sunmisola Adebayo zai jagoranci sashen Fasahar Sadarwa.
Kingdom Okere zai kasance Daraktan Harkokin Shari’a, Abiodun Dabiri Daraktan Dabaru da Tsare-tsare, CSP Richard Enemona, mai ritaya, Daraktan Tsaro da Bayanan Sirri, yayin da Aisha Abdulrahaman za ta kasance Daraktar Gudanarwa.
A cewar rahoton Daily Trust, ƙaddamar da kwamitin wani sabon mataki ne a cikin sake fasalin siyasar Obi da Kwankwaso, waɗanda suka shiga zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ne a ƙarƙashin jam’iyyu daban-daban.