Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato, arewa maso tsakiyar Najeriya, ta sanar da kama mutane 34 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, tare da kwato bindigogi 10 da harsasai 54, yayin wani samame da ta gudanar a sassan jihar.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Ayodeji Faniyan, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a shelkwatar rundunar da ke Jos, a ranar Jumma’a, 18 ga Satumbar, 2026.

Kwamishinan ya ce sun samu nasarorin ne sakamakon samun bayanan sirri da kuma haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da al’umma.

Cikin waɗanda aka kama akwai wasu da ake zargi da aikata laifin kisan kai, da garkuwa da mutane, da fashi da makami, da safarar mutane, da amfani da miyagun ƙwayoyi da kuma lalata da ƙananan yara.

Kwamishinan ya kara da cewa sun kwato bindiga kirar AK-47, da kirar GPMG, da kuma bindigogi kirar gida, tare da harsasai daban-daban a samamen da aka gudanar a Karamar Hukumar Jos ta Kudu, da Barkin Ladi, da Wase da sauran sassan jihar.

CP Ayodeji Faniyan ya ce rundunar za ta ci gaba da amfani da bayanan sirri wajen yaƙi da miyagun laifuka, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da al’ummomin jihar domin dakile ayyukan batagari da da samar da zaman lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *