Kwamitin Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayyana cewa Sudan ta Kudu ba ta samu wani ci gaba ba wajen yaƙi da cin hanci da rashawa ko tabbatar da zaman lafiyar siyasa.

Kwamitin ya bayyana haka ne bayan da ya kammala rangadin aiki a ƙasar gabanin gudanar da zaɓen farko tun bayan samun ‘yancin kai.

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta ce tana da niyyar gudanar da zaɓe a watan Disamba, shekaru 15 bayan da ƙasar ta samu ‘yancin kai.

Sai dai ƙasar da ke fama da talauci ta fuskanci ƙaruwar rikici tsakanin dakarun da ke goyon bayan Shugaba Salva Kiir da kuma jagoran ‘yan adawa Riek Machar, wanda ke tsare a gidan yari, yayin da yarjejeniyar raba madafun iko tsakanin ɓangarorin biyu ta rushe.

Kwamitin Majalisar Ɗinkin Duniya kan Haƙƙin Ɗan Adam a Sudan ta Kudu ya ce har yanzu ana ci gaba da samun manyan take haƙƙin bil’adama, ciki har da kashe-kashe, da korar mutane daga muhallansu, da cin zarafin mata ta hanyar lalata da kuma tsare mutane ba bisa ƙa’ida ba.

Kwamitin ya kuma nuna damuwa kan “rashin wani ci gaba” tun bayan wani babban rahoto da aka fitar a shekarar da ta gabata kan matsalar cin hanci da rashawa.

Rahoton ya zargi wasu manyan jami’an gwamnati da wawure biliyoyin daloli daga kuɗaɗen da ƙasar ke samu daga man fetur, yayin da kusan babu wani abin da ake yi wajen gina makarantu, asibitoci da sauran muhimman cibiyoyi.

Kwamishinan kwamitin, Carlos Castresana Fernandez, a ranar Alhamis, ya yi gargaɗin cewa, idan ba a hukunta masu take haƙƙin bil’adama ba, sannan aka karkatar da dukiyar jama’a ba tare da wani sakamako ba, hakan zai ƙarfafa al’adar rashin hukunta masu laifi, wanda daga ƙarshe ke haifar da tashin hankali.

Sudan ta Kudu ta riga ta dage zaɓen sau biyu, a shekarun 2022 da 2024, saboda gazawar gwamnati wajen gina isasshen ƙarfin hukumomi da ake buƙata domin gudanar da zaɓen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *