Ministan Yaɗa Labaran Najeriya, Mohammed Idris, ya ce kasar na duba hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwa da wani kamfanin kasar Faranshi, mai suna (France Médias Monde), mamallaka tashoshin Talabijin da Rediyo na kasar Faransa.

Ministan da yanzu haka ke ziyarar aiki a kasar ta Faransa, ya gana da Shugabar gudanarwar kamfanin, Marie-Christine Saragosse, inda suka tattauna kan hanyoyin tallafa wa harkokin watsa shirye-shiryen Faransa a Najeriya.

Tattaunawar ta mayar da hankali kan damar zuba jari, amfani da sabbin fasahohin sadarwa, ƙwarewar ma’aikatan kafafen yaɗa labarai da kuma haɓaka harkar watsa shirye-shiryen dijital a Najeriya.

Mohammed Idris  ya ce ƙarfafa haɗin gwiwa da manyan kafafen yaɗa labarai na duniya, ka iya taimakawa wajen bunƙasa bangaren labarai da shirye-shiryen a gida, tare da bude ƙarin damammaki ga ma’aikatan kafafen yaɗa labarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *